‘Yan fim da furodusoshi da daraktoci da masu ruwa da tsaki a masana’antar Kannywood sun yi ta bayyana jimami da alhinin rasuwar fitaccen dan wasan nan Umar Yahaya Malumfashi da aka fi sani da Bankaura ko Ka fi Gwamna.
A daren Talata 27 ga watan Satumba ne, Allah ya yi wa fitaccen jarumin rasuwa a wani asibiti da birnin Kano a arewacin Najeriya, bayan fama da rashin lafiya.
Umar Malumfashi da aka fi sani da sunan Bankaura a cikin tsofaffin finan-finan Hausa tun kafin kafa masana’antar Kannywood, yayin da a wannan zamanin kuma ake kiransa da sunan Yakubu ka fi gwamna, saboda rawar da ya ke takawa a shirin Arewa24 mai dogon zango wato Kwana Casa’in.
Bankaura ya taka muhimmiyar rawa domin ciyar da masana’antar Kannywood gaba, yana daya daga cikin ‘yan wasan da suka dade a wannan fagge.
Ya yi zamani da manyan iyaye mata da maza a masana’antar, irin su marigayiya Hajiya Amina Garba (Hajiya Dumba, ko Hajiyar falo), da marigayiya Hawwa Ali Dodo (Biba) da marigayiya Jamila Haruna, da su Hajara Usman, Saratu Gidado (daso) da sauran su.
An yi amanna da cewa yana daya daga cikin wadanda ke tafiya da zamani a masana’antar Kannywood, karamin misali shi ne rawar da ya taka a shiri mai dogon zango na Kwana Casa’in.
Tuni abokan sana’arsa da makusanta suka bazama shafukan sada zumunta domin bayyana alhini da ta’aziyyar rasuwarsa.
Alhaji Ado Gidan Dabino na daya daga cikinsu, musamman ganin ya na daya daga cikin wadanda sukai wa marigayin gani na karshe.
Gidan Dabino ya wallafa hotonsa tare da marigayin, a wurin daukar shirin Kwana Casa’in suna duba wasu takardu, ya wallafa.