Kashi 30 cikin dari na ‘yan ci-ranin Najeriya da ke neman mafaka a kasar Belgium ‘yan jihar Edo dake kudu maso kudancin kasar nan.
Darekta Janar na hukumar shige da fice ta Belgium, Mista Freddy Roosemont ne ya bayyana haka a wajen wani taro da hukumar tare da hadin gwiwar kungiyar Pathfinder Justice Initiative (PJI), ta shirya a Benin, babban birnin jihar Edo, a yau Laraba.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito, cewa Mista Roosemont ya bayyana batun neman mafaka da ‘yan Najeriya ke yi a Belgium da cewa abin damuwa ne matuka.
Ya ce kashi 30 cikin dari na masu neman mafakar daga jihar Edo suke, sai kashi 20 ciki dari daga jihar legas, yayin da sauran kashi 50 kuma suke daga wasu jihohin kasar nan.
Jami’in ya ce yawan ‘yan jihar Edo da ke da hannu a safarar mutane idan aka kwatanta da sauran ‘yan jihohin Najeriya, shi ya tilasta musu shirya wayar da kan jama’a kan tafiya ci-rani waje ta hanyoyin da suka dace.
Babban Daraktan ya ce a shekara ta 2022 kusan ‘yan Najeriya 370 suka nemi mafakar, sannan kuma a shekara ta 2023 kusan 360 ne suka nema.
Roosemont ya shawarci ‘yan Najeriya da su daina bari ana yaudararsu da sunan taimaka musu samun aiki a Belgium, domin guraben ayyukan a can su ma a cike suke.
Ya ce a halin yanzu akwai ‘yan Najeriya kusan 5,000 da ke zaune cikin ka’ida a Belgium.
Darektan ya ce wasu daga cikin ‘yannajeriyar sun je Belgium din ne ta hanyar ka’ida wasu kuwa sun bi ta haramtacciyar hanya mai hadari ta tekun Bahar Rum.