fidelitybank

‘Yan Jaridu sun kaurace daukar rahoton gwamnan Kano

Date:

Ƙungiyar wakilan kafafen yaɗa labaru da ke ƙarƙashin ƙungiyar ƴan jarida ta Najeriya reshen jihar Kano ta ce za ta ƙaurace wa bayar da rahoto kan duk wasu ayyukan gwamnatin jihar daga yau Litinin.

Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a wata sanar da ta fitar yau, wadda ta samu sa hannun shugaban ƙungiyar, Aminu Ahmed Garko.

Sanarwa ta ce ta ɗauki matakin ne sanadiyyar cin zarafin da jami’an gwamnatin jihar ta Kano ke yi wa wakilanta a lokacin da suke gudanar da ayyukansu.

Sanarwar ta ce “duk wani yunƙuri da aka yi na tattaunawa da gwamnati da jami’anta domin warware matsalolin abin ya ci tura”.

Sanarwar ta ci gaba da cewa wakilan kafafen yaɗa labarun sun ci gaba da fuskantar “hantara da tsangwama har ma da duka a lokacin da suke gudanar da ayyukansu”.

Daga nan sai sanarwar ta ce ƴan jaridar ba za su sake ɗaukan rahoton duk wani taron manema labaru, ko ayyukan gwamnati ko tattaunawa da jami’an gwamnatin ba har sai gwamnatin jihar ta ɗauki alƙawarin kare ƴanci da lafiyar ƴan jarida.

Najeriya na daga cikin ƙasashen da ake wa kallon masu rauni wajen kare hakkin ƴan jarida.

A cikin rahotonta na shekara ta 2023, ƙungiyar kare hakkin ƴan jarida ta Reporters Without Borders ta ce ƴan siyasa a ƙasashe irin Najeriya na amfani da ƙarfinsu wajen daƙile ayyukan ƴan jarida, yayin da kuma wasu ƴan siyasar ke kafa nasu kafafen yaɗa labarun domin yaɗa farfaganda da labaran bogi.

nigerianewspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp