Wasu ‘yan fashi da makami a ranar Talata sun kashe mutane uku a karamar hukumar Birninkudu da ke jihar Jigawa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar DSP Lawan Shiisu ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Dutse.
“A ranar Talata da misalin karfe 8:00 na dare ne aka samu labari daga kauyen Iggi cewa an hangi wasu ‘yan bindiga uku a kan babur daya a yankin Iyayi na jihar Bauchi, inda suka tunkari kauyen Iggi da ke karamar hukumar Birninkudu ta kauyen Babuwawa.
“Bayan samun labarin, an hada tawagar ‘yan sintiri zuwa yankin, kuma an sanar da duk masu ruwa da tsaki a harkar tsaro, musamman ‘yan banga.
“Da misalin karfe 10:15 na dare ne aka samu kiran tashin hankali daga bangaren Warwade na Birninkudu cewa ‘yan bindigan sun kwace babur daga hannun wani da ba a san ko su wanene ba,” inji shi.
A cewarsa, ‘yan fashin da ake zargin sun yi harbi da dama kan wata mota da ta zo dauke da fasinjoji hudu, inda ya kara da cewa ‘yan fashin sun harbe direban, Hassan Garba daya da fasinjoji biyu, mai suna Garba Maiwake da Shehu Saidu.
Kakakin ya ce an ajiye gawarwakin ne a dakin ajiye gawa na Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Birninkudu, inda ya kara da cewa rundunar ta zafafa sintiri domin cafke wadanda ake zargi da gudu.