fidelitybank

Yan fashi sun farwa unguwar Zangon Gabas a Kano

Date:

Al’ummar unguwar Zangon Gabas dake yankin karamar hukumar ungoggo a jihar kano, sun tsinci kan su a cikin halin rudani, gami da firgici a sakamakon yadda guggan wadansu bata garin matasa da ake zargin yan fashi da makamai ne, sun tsallaka gidajen mutane yankin cikin tsakiyar dare.

Guda daga cikin matasan mai suna Daddy wanda ake zargin shi ne ke jagorantar sauran matasan na kara cigaba da cin karan su babu babbaka a sassan unguwanin baki dayan ta. Rahotanni sun nuna cewa a ranar Asabar din da ta gabata sai dashi Daddy ya jagoranci wasu matasan dauke da wasu muggan makamai da suka hadar da Wukake, Almakashi, da kuma tukunyar iskar Gas suka shiga gidajen wasu mazauna unguwar ta zangon Gabas .

Malam Umar Gausu guda ne daga cikin magidanta da bata garin matasan, suka kulle su a cikin ban dakin cikin gidan su, wanda kuma kafin wannan lokacin sai dashi Daddy yayiwa matar sa mai suna Zaliha Umar Gausu awon gaba da makudan kudaden masu ya awon gaske.

Malam Muhammad Ahamd da kuma Malam Suleman Musa sun bayyana Kadaura24 cewar, babban abunda ya kara tayar musu da hankalin shi ne yadda matasan ke rike da muggan makamai a hannayen nasu da kuma tukunyar Iskar Gas, wanda da zarar kayi musu tirjiya wajan mika abunda suka bukata daga gare ka suke bankawa mutum wuta.

Koda yake a wani binkecan da kadaura24 ta gudana ta gano cewar wannan bashi karon farko ba dashi WaÉ—anan Matasa suke shiga hannun yan bijilantin idaban-daban, amma wane tudu wane zangare ake hawa daga bisani wanda ake zargin sai ya sake fitowa.

Yanzu haka dai kwamitin tabbatar da tsaro a yankin sun yi yinkuri domin kawo karshen wannan matsala, kwamitin karkashin jagorancin Alhaji Hamza Haruna ya bayyanawa manema labarai cewar tun a shekarun baya, ire iran matasan ne suka addabe su wajen tsallakawa gidajensu da jakar Man fetur da kuma na’urar cirar kudi ta tafi da gidan ka wato P.O.S a turance.

A cewar Alhaji Hamza Haruna biyo bayan gudanar da wani sumame na musamman da yan kwaminitin tabbatar da tsaron unguwar ta zangon Gabas suka yi, yanzu haka sun sami nasarar kama Daddy tare da mika shi zuwa ga rundunar yan sanda ta jihar kano, domin fadada bincike akan sa.

Yan Kwamitin sun kuma sha alwashi bibiyar wannan alamarin har zuwa gaban kuliya domin ganin matashin ya girbe abunda ya shuka.

opra news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp