Wasu ƙarin ƴan fafutuka a Nijar na zaman durshen a Yamai, babban birnin ƙasar kan takunkumin da ƙugiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afrika ta yamma ECOWAS ta kakaɓa wa ƙasar tun bayan juyin mulki.
Manufar wannan zamar shine tillastawa ƙungiyar ECOWAS cire wannan takunkumi.
ƙungiyar Ecowas dai ta sanya wa Nijar takunkumin tattalin arziƙi da kuma rufe harkokin kasuwanci na kan iyaka da Nijar a yunƙurin matsa wa shugabannin juyin mulkin kasar lamba har sai sun mayar da mulkin dimokradiyya.
Shugaban Najeriyar, Bola Tinubu, wanda kuma shi ne jagoran Ecowas, ya bayyana taka-tsantsan wajen mu’amala da Nijar saboda damuwar da ake da ita dangane da hamɓaras da Shugaba Bazoum daga kan mulki.
Gwamnatin mulkin soja a Nijar dai ta ce za ta miƙa mulki bayan shekara uku hannun farar hula.


