fidelitybank

‘Yan daban da suka tayar da rikici a gidan gwamnatin Kano suna hannun ‘yan sanda

Date:

Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta cafke mutum takwas da ake zargi da yunƙurin kawo tarnaƙi a bikin ƙaddamar da sabbin kwamishinoni da aka yi a baya-bayan nan.

Kakakin rundunar ƴan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, cikin sanarwar da ya wallafa a shafinsa na fesbuk, ya ce an kama mutanen ne da ke bayyana kansu a matsayin magoya bayan ɗaya daga cikin ƴan siyasa da ke neman barazana ga doka da oda.

Kwamishinan ƴan sanda CP Usaini Gumel ya gargarɗi ƴan jagaliya da masu tallafa masu da su guji tayar da zaune tsaye inda ya ce “za a kama duk wani da ke son haifar da barazana ga tsaro da zaman lafiya a wurin da ake gudanar da tarukan gwamnati, sannan zai fuskanci hukuncin abin da ya aikata.”

Sanarwar ta ce mutanen da aka kama a yanzu na sashen binciken manyan laifuka inda ake gudanar da bincike mai zurfi domin hukunta su bisa tanadin doka.

Rundunar ta ce ta ɗauki matakin ne domin tabbatar wa al’ummar jihar cewa ana ɗaukan matakan da suka dace na hana duk wani abu da zai kawo hargitsi da barazanar tsaro a sassan jihar Kano.

breaking news in nigeria today punch

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp