fidelitybank

‘Yan cirani sun daskare a dusar kankara

Date:

Akalla wasu ’yan ci-rani 12 ne da ke kokarin tsallakawa kasashen Turai aka tsinci gawarwakinsu, bayan sun daskare a dusar kankara a kan iyakar kasashen Turkiyya da Girka.

Rahotanni sun nuna cewa, ko sutturar kirki babu a jikin mutanen da aka gano gawarta su.

Ministan Harkokin Cikin Gida na Turkiyya, Suleyman Soylu, ya wallafa hotunan mutanen, a shafin Twitter, shimfide a gefen hanya a kusa da garin Ipsala da ke Arewa maso Yammacin kasar, suna sanye da gajerun wanduna da rigunan T-shirt, duk da sanyin da ake fama da shi.

Ya yi zargin cewa, mutum 12 na daga cikin dimbin wadanda kasar Girkar take yi wa korar kare.

“12 daga cikin ’yan ci-rani 22 da Girka ta kora sun daskare a dusar kankara sannan suka mutu, bayan an cire musu sutturarsu da takalma,” inji Ministan.

Tsananin sanyi dai a yankin ya kai kusan tsakanin digiri biyu zuwa uku a ma’aunin celcius da daddare a karshen watan Janairu da kuma farkon Fabrairu.

Minista Suleyman ya zargi masu tsaron iyakar na Girka da nuna rashin imani a kan mutanen, inda ya kuma ce Tarayyar Turai na da rauni matuka.

Ita kuwa a nata bangaren, kasar Girka, ta bakin Ministan Shige da Fice na kasar, Notis Mitarachi, ta bayyana lamarin a matsayin babbar masifa, amma ta zargi Turkiyya da siyasantar da lamarin.

Hukumar Kula da Shige da Fice ta Majalisar Dinkin Duniya (IOM) dai ta ce ita ma ta kadu matuka da jin labarin mutuwar mutanen.

Wani rahoto da Hukumar Kula na ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ya kiyasta cewa sama da mutum 2,500 ne ko dai suka mutu ko kuma suka bace a kokarinsu na tsallakawa Turai daga Arewacin Afirka da Turkiyya a shekarar 2021 kawai. A cewar Aminiya.

nnnhausa

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp