‘Yan cirani 41 sun mutu bayan da jirgin ruwan da suke ciki ya tarwatse a tsuburin Lampedusa da ke Italiya.
Wasu mutum huɗu – da suka tallake rijiya da baya a hatsarin – sun faɗa wa masu aikin ceto cewa, jirgin nasu ya taso ne daga tashar jirgen ruwa na Sfax a Tunisiya, sannan ya nutse a kan hanyarsa ta zuwa Italiya.
Fiye da mutum 1,800 ne suka rasa rayukansu a wanna shekara a kokarinsu na shiga Turai daga yankin Arewacin Afirka.
Hukumomin Tunisiya sun ce tashar jiragen ruwa ta Sfax – wanda ke da nisan kilomita 130 daga tsuburin na Lampedusa – ya zama wata kafa da ‘yan cirani ke amfani da ita wajen shiga Turai.
A baya-baya nan masu gadin teku da ƙungiyoyin agaji sun kuɓutar da mutum 2,000 da suka isa tsuburin Lampedusa. In ji BBC.