Gwamnatin jihar Neja ta sanar da sakin wasu ‘yan kasar China 7 da aka yi garkuwa da su a unguwar Ajata-Aboki da ke karamar hukumar Shiroro a jihar.
Wadanda abin ya shafa, wadanda aka samu ‘yancinsu ta hanyar aikin ceto da rundunar sojin saman Najeriya, NAF ta yi, an sace su ne a watan Yunin 2022.
Gwamnatin ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan tsaro na cikin gida da ayyukan jin kai, Hon. Emmanuel Bagna Umar in Minna.
A cewarsa, “muna samun rahotannin farin ciki matuka game da aikin ceto da NAF ta yi wajen ceto ‘yan kasar China 7 da aka yi garkuwa da su. Mai Girma Gwamna Abubakar Sani Bello, ya yabawa kwazon kwamandan da sojojin runduna ta 271 NAF Detachment na wannan gagarumin aikin.
“Musamman ya yaba da salon jagoranci da basirar hafsan hafsan sojin sama, Air Marshal Oladayo Amao, wanda a karkashin jagorancin NAF ta ci gaba da samun gagarumar nasara a ayyukanta a fadin kasar, ciki har da nasarar ceto wadannan ‘yan kasar China a Kampanin Doka, Gwaska area of Birnin Gwari LGA, Kaduna State”.
Ya kuma bayyana cewa gwamnatin Neja a karkashin jagorancin Gwamna Sani Bello za ta ci gaba da hada kai da duk jami’an tsaro a jihar domin tabbatar da ‘yan kasa suna cikin koshin lafiya.
Umar ya kara da cewa, “Gwamna Bello yana taya wadanda abin ya shafa, iyalansu, abokansu da abokan huldar su domin ceto su da kuma yi musu fatan alheri”.


