Wasu da ake zargin ƴan ƙungiyar Boko Haram sun yi awon gaba da wani Farfesa na jami’ar sojoji ta Najeriya da ke garin Biu tare da wasu fasinjoji.
Ƴan bindigar sun kama mutanen ne kan hanyar Damaturu zuwa garin Biu kusa da garin Kamuya.
Wannan lamari dai ya tayar da hankalin jama’a a cikin jami’ar da kuma garin na Biu.
Sai dai duk ƙoƙarin da aka yi domin ji daga ɓangaren ƴansandan jihar ta Borno bai yi nasara ba.
Ita dai wannan hanyar ta kasance ɗaya daga cikin waɗanda aka fi yin garkuwa da jama’a a yankin sakamakon rashin kyawunta, a cewar al’ummar yankin.