Daruruwan ‘yan ta’adda, masu aikata laifuka da masu safarar muggan kwayoyi sun tsere daga gidan yarin Koutoukalé a Jamhuriyar Nijar.
Gidan yarin da ke kusa da babban birnin Yamai, ya kasance wurin da aka yi tashe-tashen hankula a ranar alhamis din da ta gabata, wanda ya mamaye masu gadi tare da barin fursunonin tserewa da makamai da motoci.
A cewar shaidun gani da ido, da tsakar rana ne aka rika jin karar harbe-harbe da fashe-fashe a cikin gidan yarin, lamarin da ya sa jami’an tsaro suka mayar da martani cikin gaggawa.
Sai dai kuma an bayyana cewa, fursunonin sun riga sun sami galaba a gidan yarin, inda suka yi ta kutsawa ta kofofin sulke, da shingen waya, da ramuka.
An tattaro cewa an dakile yunkurin kai hari a gidan yarin sau biyu a baya.
An bayar da rahoton cewa, ministan cikin gida na kasar ya fitar da sakon rediyo ga dukkan gwamnonin, inda ya tabbatar da guduwar tare da yin kira ga sarakunan kauyuka da shugabannin addinai da su kai rahoton duk wani mutum da ake zargi.
An kafa dokar hana fita a yankin Tillabéri, kuma duk yankin kogin Neja na cikin shirin ko ta kwana.


