Gwamnan Katsina Umaru Dikko Radda ya ce galibin ‘yan bindigar da suka addabi jiharsu ‘yan asalin jihar ne ba wai baƙi ba.
Gwamna Radda ya shaida hakan ne a wata tattaunawa da kafar talabijin ta Channels a Najeriya kan matsalolin tsaro da hanyoyin kawo karshen ‘yanbindiga.
Ya ce galibin ‘yan bindigar sun fito ne daga asalin yankunan da matsalolin tsaron ya addaba. Kuma mun san iyayensu da kakaninsu kuma tare muke rayuwa, in ji Dikko.
A cewarsa, matsalolin tsaron sun tilastawa gwamnatinsa kafa jami’an tsaron sa-kai a yankunan domin taimaka musu wajen samun sauki.
Dikko Radda ya ce abu ne mai sauki ba, amma suna cigaba da aiki da al’umomin waɗannan yankunan wajen sake fahimtar matsalolin domin ganin yadda za a daƙile matsalar baki ɗaya.
A cewar gwamnan, babu wani cigaba da za a samu a yankunan da matsalolin tsaron ya addaba muddin ba a samu sauƙin yanayin da ake ciki ba.