Ƴanbindiga sun kashe wasu mutum 38 ta hanyar yi musu yankan rago, daga cikin mutum 56 da suka yi garkuwa da su sakamakon gaza biyan kuɗin fansa da ƴanbindigar suke nema.
Mutanen da aka kashe ɗin sun kasance ƴan ƙauyen Banga da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar ƙauran Namoda da ke jihar Zamfara.
Shugaban ƙaramar hukumar, Manniru Haidara Ƙaura wanda ya shaida wa BBC yadda al’amarin ya faru, ya ce yawancin waɗanda aka yi wa yankan ragon matasa ne.