Ƴanbindiga da suka yi garkuwa da ɗaliban makarantar samun ƙwarewar a aikin lauya da aka sace a jihar Benue sun ce, idan ba a biya kuɗin fansa ba, za ku kashe su, kamar yadda kafar The Punch ta ruwaito.
An sace ɗaliban ne a ranar 26 ga watan Yulin a hanyarsu ta zuwa makarantar domin samun horo da ke Yola a jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin ƙasar daga jihar Anambra da ke kudu maso gabashi.
Kafar ta Punch ta ruwaito daga wata majiya cewa masu garkuwar sun ƙara kuɗin fansar daga dala 13,110 zuwa dala 32,688 kan kowane ɗalibi, sannan suka yi barazanar kashe ɗaliban matuƙar ba a biya kuɗin ba.
“Sun ce idan ba mu kawo kuɗin ba, za su kashe su, sanan sun gargaɗe mu kada mu saka jami’an tsaro a maganar.”
Kakakin runduar ƴansandan jihar Adamawa, Yahaya Suleiman ya ce suna aiki tare da rundunar jihar Benue domin ceto ɗaliban.