Wasu masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da mutane 11 a wani yankin babban binrijn tarayya Abuja.
Rahotonni sun nuna cewa, daga cikin wadanda aka sacen, akwai matar mataimakin shugaban PDP na wani yanki, lamarin da ya jawo tashin hankali, yayin da ‘yan bindigan suka nemi dangin su biya makudan kudade kafin su sako mutanen 11.
Matar mai suna, Asabe Mohammed Koriya, matar mataimakin shugaban jam’iyyar PDP a gundumar Gwargwada a karamar hukumar Kuje a Abuja. An sace ta ne tare da wasu mutane 10.
Dan uwan ​​daya daga cikin wadanda abin ya shafa, Salihu Ibrahim ya ce, lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da misalin karfe 5 na yamma a mahadar Gwargwada da Gwombe daura da unguwar Rubochi.