fidelitybank

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da matafiya a hanyar Zamfara zuwa Funtua

Date:

Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan ta’adda ne, sun kai wani samame a kan hanyar Zamfara zuwa Funtua, inda suka yi garkuwa da dimbin matafiya da ke tafiya zuwa wurare daban-daban na kasar nan.

A cewar wani ganau, Mista Nura Ola Tsafe, ‘yan ta’addan sun gudanar da samamen ne a ranakun Juma’a da Asabar a wurare daban-daban da ke tsakanin Gusau- Gidan Dawa-Yandoto Daji a karamar hukumar Tsafe.

Ya ce an fara gudanar da ayyukan ne a ranar Juma’a, kuma ‘yan bindigar sun ci gaba da munanan ayyukansu har zuwa ranar Asabar, inda ya ce an kai wadanda aka sace zuwa dajin.

Karanta Wannan: Zamfara ta kori kungiyoyi masu zaman kansu daga jihar

“Shahararrun ‘yan bindigar sun yi awon gaba da fasinjojin da ba su ji ba ba su gani ba a hanyarsu ta zuwa halartar Mauludin Musulunci. ‘Yan ta’addan sun yi garkuwa da wasu fasinjojin motocin kasuwanci guda biyu a tsakanin Yandoton Daji da Kwatarkwashi,” inji shi.

Ya kuma kara da cewa ‘yan bindigan sun kuma kai wa wasu mazauna garin Tsafe hari a ranar Juma’a a kan Yandoton Daji-Gidan Dawa, inda ya kara da cewa wadanda harin ya rutsa da su sun tsere da kyar ne sakamakon shiga tsakani da sojojin suka yi.

Nura Tsafe ya koka da yadda irin wadannan ayyuka a kan titin Gusau zuwa Funtua ya zama abin damuwa musamman a yanzu da al’ummar kasar ke shirin tunkarar babban zabe na 2023.

Idan dai za a iya tunawa, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Kolo Yusuf tare da tawagarsa ta ‘yan Tactical, sun gudanar da wani samame a kan hanyar Zamfara zuwa Funtua domin kara tabbatar da tsaro a hanyar da kuma karfafa kwarin gwiwar matafiya.

tribune news paper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp