‘Yan bindiga sun yi garkuwa da ɗaliban Jami’ar Nsukka da ke Jihar Enugu, yayin da suke komawa makarantar bayan dawowa daga yajin aiki.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 4:00 na yammacin Lahadi a yankin Ƙaramar Hukumar Igbo-Etiti. Sai dai babu tabbaci game da yawan ɗaliban da aka sace zuwa yanzu.
Kafar yaɗa labarai ta Premium Times ta ruwaito cewa ‘yan bindigar sun shafe tsawon lokaci suna yin garkuwa da matafiya a hanyar tun daga ranar Asabar.
Wasu majiyoyi sun ce an ci gaba da kai hare-haren har zuwa ranar Talata.
Ɗalibai a jami’o’in gwamnatin Najeriya na komawa makarantu a makon nan bayan ƙungiyar malamai ta ASUU ta janye yajin aikin da ta shafe wata takwas tana yi game da walwalarsu da suka zargi gwamnatin ƙasar da ƙin kulawa.