fidelitybank

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai 4 a Ondo

Date:

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da wasu dalibai hudu na kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kogi a jihar Ondo.

‘Yan bindigar sun yi garkuwa da daliban ne a kan babbar hanyar Akunnu zuwa Ajowa a yankin Akoko North West na jihar Ondo.

An ce wadanda lamarin ya rutsa da su na kan hanyarsu ta komawa gida ne domin bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara a lokacin da ‘yan bindigar suka yi wa motar da suke ciki hanya.

Bayan faruwar lamarin, al’ummar Ajowa da daliban ke tafiya sun jefa su cikin firgici da tada jijiyoyin wuya tsakanin iyaye da sauran al’umma.

Wata majiya a unguwar ta shaida wa wakilinmu cewa, an yi garkuwa da mutanen ne a lokacin da suke dab da isa wurin da suke Ajowa.

Majiyar ta kara da cewa har yanzu masu garkuwa da mutanen ba su tuntubi ko daya daga cikin iyalan daliban da aka sace ba.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kwamandan ‘yan sanda a Ikare-Akoko, ACP Muri Agboola, ya bayyana cewa mutanensa sun yi ta tseguntawa dazuzzukan da ke kan hanyar Akunnu-Ajowa Akoko domin ceto daliban da aka sace.

general news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Hisbah za ta yi wa ‘yan Daban Kano aure

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta sanar da wani...

Ganduje ya dawo Najeriya bayan ya shafe wata guda a Landan

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Ganduje,...

Barrister Sa’idu ya kama aiki bayan ya maye gurbin Muhyi Magaji

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya rantsar...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

Barau zai mayar da filin wasan BUK na zamani

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya...

Jami’ar Bayero ta Kano ta yi sabon shugaba

Farfesa Haruna Musa, ya karɓi ragamar shugabancin jami’ar Bayero...

Gwamnatin Kano ta amince Barau FC ta yi wasa a filin Sani Abacha

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kungiyar kwallon kafa...

Gwamnatin Tinubu na takalar Kwankwaso da fada – Buba Galadima

Jigo a jam'iyyar NNPP, kuma na hannun tsohon gwamnan...

Newcastle United ta dauki dan wasan tsakiya Jacob daga Aston Villa

Newcastle United ta sanar da daukar dan wasan tsakiya...

Hisba ta kama ‘yan Mata 62 da zargin aikata baɗala a Kano

Hukumar Hisbah ta kama mutane 62 kan zargin aikata...
X whatsapp