Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da akalla yara 30 a kauyen Kasai da ke karamar hukumar Batsari a jihar Katsina.
Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa Batsari na daya daga cikin kananan hukumomin tsaro na gaba-gaba a jihar inda ayyukan ‘yan fashi, da sauran masu aikata laifuka ke karuwa kusan kullum.
Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, gwamnati da hukumomin tsaro ba su ce uffan ba kan batun.
Wani mazaunin yankin ya shaidawa gidan talabijin na Channels a wata wayar tarho cewa sabon harin da aka kai kan yaran ya faru ne da sanyin safiyar ranar Litinin.
Shi ma jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq, shi ma har yanzu bai mayar da martani kan wannan batu ba.