Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sake yin garkuwa da wani Dokta Bello Janvako, Darakta a Cibiyar Bincike ta Jami’ar Tarayya ta Gusau a Jihar Zamfara.
An yi garkuwa da Janbako, wanda kuma babban malami ne a Sashen Nazarin Addinin Musulunci na Jami’ar, a gidansa da ke Unguwar Damba a Gusau, a daren Laraba.
Wani mazaunin yankin mai suna Muhammad Ibrahim ya ce ‘yan ta’addan sun kai farmaki gidan Janbako da misalin karfe 1:30 na safiyar Laraba inda suka tafi da shi.
Ibrahim ya ce an yi musayar wuta mai tsanani tsakanin ‘yan bindigar da jami’an tsaro a wani yunkuri na dakile sace babban malamin ba tare da samun nasara ba.
Ya ce, “Lokacin da ‘yan bindigan suka isa gidan Bello Janbako, sun yi harbin bindiga da dama don tsorata mazauna yankin.”
“‘Yan fashin sun kutsa cikin gidan ne daga inda aka sace shi amma jami’an tsaro da suka isa yankin a aikin ceto sun kalubalanci shi.”
“Jami’an tsaro sun fatattaki ‘yan bindigar amma abin takaici, sun kasa kubutar da malamin jami’ar.
Idan dai za a iya tunawa, an sace wani mazaunin yankin wanda darakta ne a ma’aikatar kudi ta jihar, Malam Sabiu kwanaki biyu kafin nan.
An sace matar da ’ya’yan wani daraktan kudi, Surajo Hassan, wadanda su ma mazauna yankin ne a bara.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Yazid Abubakar bai samu damar jin ta bakinsa ba har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto.