Rahotanni daga Jihar Kaduna na cewa wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun sace ɗalibai da wasu matafiya a kan hanyar Birnin-Gwari.
Jaridar Vanguard a Najeriya ta ruwaito cewa kuma sun ƙona motoci takwas waɗanda ke jigilar ɗalibai domin rubuta jarrabawa a kwalejin horas da aikin kiwon lafiya ta Makarfi.
Rahotanni sun ce maharan sun yi kwanton-ɓauna a wurare uku kan babbar hanyar waɗanda suka rinƙa tursasa motoci suna juyawa.
Waɗanda suka faɗa tarkon maharan a ƙarshe an yi garkuwa da su. Sai dai jami’an tsaro ko hukumomi a jihar ba su yi ƙarin bayani kan lamarin ba