Wani hari da ‘yan bindiga suka kai wa matafiya ranar Laraba da maraice a kan babbar hanyar da ke tsakanin Kucheri zuwa Gusau a jihar Zamfara, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
Baya ga salwantar rayukan fasinjoji, ‘yan bindigar sun kuma sace wasu ƙarin mutane.
Daga cikin waɗanda harin ya rutsa da su har da tsohon ɗan majalisar wakilai ta tarayya daga jihar ta Zamfara, Alhaji Kabiru Classic.
A hirarsa da Zubairu Ahmad Kasarawa, ya shaida masa yadda lamarin ya rutsa da su.