Aƙalla mutum 40 ne aka sake kashewa a wani hari da wasu mahara suka kai a garin Zike da ke yankin Kwall a ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Filato.
Mai bai wa gwamnan jihar Filato shawara kan harkokin tsaro Admiral Shipi Gakji mai ritaya ya tabbatar wa BBC cewa an kai harin ne a cikin dare, wayewar garin yau Litinin.
Bayanai sun nuna cewa maharan sun buɗe wuta kan mai uwa da wabi a lokacin da suka shiga ƙauyen.
Gakji ya shaida wa BBC cewa “E haka ne, an kai harin, muna ƙoƙarin haɗa yawan mutanen da aka kashe, amma tabbas yawan ya kai haka ɗin (40).”
Wannan na zuwa ne kimanin mako ɗaya bayan wani hari da ƴan bindiga suka kai a ƙaramar hukumar Bokkos ta jihar ta Filato, wanda ya yi sanadin kashe fiye da mutum 50 da tarwatsa wasu da dama.
Filato jiha ce mai al’umma masu mabambantan ƙabila da addini, wadda ta daɗe tana fama da rikici mai nasaba da addini da kuma ƙabilanci.
Sau da yawa akan zargi makiyaya da laifin kai irin waɗannan hare-hare, sai dai a lokuta da dama sukan musanta hakan.
Hukumomi a baya sun sha kafa kwamitoci domin magance matsalar, amma duk da haka, lamarin ya ci tura.