fidelitybank

‘Yan bindiga sun sace mutane da dama a Abuja

Date:

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a unguwar Dawaki da ke yankin babban birnin tarayya Abuja inda suka sace mutane 13, amma kuma daga bisani jami’an tsaro sun ceto hudu daga cikinsu bayan sun yi artabu.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC cewa ‘yan bindigar sun fara zuwa ne suka sace mutum hudu, amma mutanen suka tsere, daga bisani kuma suka sake kama mutum 13, a harin wanda aka kai ranar Lahadi da daddare

Bayan sun kama mutanen ne jami’an tsaro suka kai dauki inda suka yi artabu da su a kusa da madatsara ruwa ta Usman Dam, inda suka nasarar ceto mutum hudu daga cikin 13.

Sai dai kuma wasu rahotannin na cewa mutanen da aka sace sun kai 20.

Sai dai kuma a wata sanarwa da rundunra ‘yansanda ta Abuja ta fitar, mai magana da yawun rundunar SP Josephineb Adeh ta tabbatar da aukuwar satar mutanen.

Sai dai sanarwar da ‘yansandan suka fitar wadda a ciki suka ce da hadin kai da mafarauta suka yi wa barayin kwanton-bauna a tsaunin Ushafa daga Bwari, ba ta bayyana yawan mutanen da aka sace ba.

Amma kuma ‘yansandan sun ce sun yi nasarar ceto mutanen tare da tarwatsa ‘yan bindigar da suka ce sun tsere da raunukan bindiga.

Sanarwar ta kara da cewa yayin da daya daga cikin wadanda aka ceto yake kwance a asibiti ake masa magani, jami’an na ci gaba da bincike domin gano sauran mutanen da aka sace wadanda suka tsere yayin musayar wuta da barayin.

vgn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp