Rundunar ‘yan sandan jihar Edo, tabbatar da sace wasu mutum biyu da ake zargin wasu ‘yan bindiga sun sace a ƙaramar hukumar Owan ta Yamma.
Rundunar ta ce, tana bakin ƙoƙarinta dan ganin ta kama masu garkuwa da mutanen tare da kuɓutar da mutanen da aka sacen.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito ‘yan sanda na cewa, mutanen biyu da aka sace masu suna Omafuaire da kuma Folorunsho, sun je gonarsu ne da ke Ugbokuli, domin tsinko kwakwar manja a lokacin da ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su.
Karanta Wannan: ‘Yan bindiga sun harbe mai kula da cocin ECWA a Kaduna
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar SP Childi Nwabuzor, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce suna kan bincike domin gano tare da kuɓutar da mutanen.