Wasu ‘yan bindiya dauke da makamai sun kai hari kauyen Gidan Bakuso da ke yankin karamar hukumar Gada a jihar Sokoto, tare da sace daliban wata tsangaya.
Rahotonni na cewa maharan sun far wa garin ne da tsakar daren ranar Juma’a lokacin da daliban ke barci.
Dan majalisar tarayyar mai wakiltar yankin, Honarabul Bashir Usman Gorou ya tabbatar wa BBC faruwar harin, inda ya ce kimanin dalibai 15 ne ‘yan bindigar suka sace, da wasu mata hudu.
Ya ce daliban almajirai ne na makarantar Allo wadanda shekarun suka kama daga takwas zuwa 14.
Baya ga daliban tsangayar, dan majalisar ya ce a yanzu haka akwai fiye da mutum 63 a yankin da ke hannun ‘yan bindiga, to amma wannan shi ne karo na farko da ake sace kananan almajirai a yankin.
Harin dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin jihar ke kaddamar da jami’an sa kai na tsaro don magance matsalar tsaron a jihar.
A baya-bayan nan ‘yan bindiga sun zafafa kai hare-hare tare da sace mutane masu yawa a wasu yankunan arewacin Najeriya.
Ko a ranar Alhamis da ta gabata ma wasu ‘yan bindiga dauke da makamai suka kai hari makarantar furame da karamar sakandiren Kuriga a jihar Kaduna, tare da sace daliban makarantar kimanin 287.
Haka ma makon da ya gabata wasu mahara suka sace wasu mutane mazauna sansanin ‘yan gudun hijira fiye da 100 galibinsu mata da kananan yara a lokacin da suke neman itacen girki a garin Gambouro Ngala a jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin kasar


 

 
 