Rahotanni daga jihar Filato na nuni da cewa wasu ‘yan bindiga sun sace wani basarake a jihar.
Basaraken mai suna Da Gyang Balak, wanda ya kasance mai fada aji a gundumar Vwang da ke karamar hukumar Jos ta Kudu.
Dan Majalisar da ke wakiltar karamar hukumar a majalisar dokokin jihar ne ya tabbatarwa da jaridar Punch, cewa a ranar Lahadi da karfe 8 na dare a ka sace basarake.
Rahotanni sun ce an sace shi ne a lokacin da ya ke kan hanyarsa ta komawa gida a kan titin da ke yankin Kuru.
Lamarin ya faru ne kasa da wata guda, bayan da wasu ‘yan bindigar su ka sace wani basarake a karamar hukumar Mangu wanda daga bisani suka sake shi bayan biyan kudin fansa.