Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a unguwar Keta da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara inda suka kona motoci 11 da shaguna uku.
Harin wanda ya auku da rana tsaka, ya kuma ci rayukan mutum guda.
Wani mai sharhi kan harkokin tsaro, Bakatsine ne ya bayyana lamarin a shafinsa na X ranar Lahadi.
A cewarsa, maharan dauke da makamai sun afkawa al’ummar yankin, inda suka yi ta lalata da su kafin su gudu.
Bakatsine ya rubuta cewa: “Da rana tsaka wasu ‘yan bindiga sun kai hari a unguwar Keta da ke karamar hukumar Tsafe, jihar Zamfara, inda suka kona motoci 11 da shaguna uku.