Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kashe jami’an ‘yan sandan uku a jihar Neja.
Jami’an tsaro sun yi wannan kiran ne a lokacin da suke amsa kiran gaggawa a ranar Alhamis, 12 ga watan Mayu, kamar yadda kafar yada labarai ta Naija ta ruwaito.
Da yake bada rahoton lamarin, Aminiya ta tabbatar da cewa maharan da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun bindige jami’an ‘yan sanda uku da wani direban babur ne a Suleja a ranar Alhamis da misalin karfe 11 na dare.
Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun yi wa jami’an tsaron kwanton bauna ne da watakila suna jiran jami’an tsaro a kusa da wani wuri da ake kira Old Barrack.
An bayyana sunayen jami’an da aka kashe kamar haka; SGG Hosea Saba, CPL Yahaya Yakubu da PSC Aminu Sani, dukkansu ma’aikatan B Division Suleja ne.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Shugaban Majalisar Suleja, Abdullahi Shuaibu Maje, ya ce kimanin mutane uku ne suka tsira daga harin, ciki har da dan banga.