Rundunar ‘yan sandan jihar Rivers, a ranar Alhamis ta ce wasu ‘yan bindiga da ba a tantance ba sun kashe daya daga cikin jami’anta, Sunday Baba.
Rundunar ‘yan sandan ta fitar da takaitaccen bayani a kan ta a ranar Alhamis, inda ta ce Mista Baba, wani sufeton ‘yan sanda, wanda ya yi aiki a yankin Rumuolumeni na jihar, ya rasa ransa a bakin aiki ranar Laraba.
“Abin bakin ciki ne cewa zama dan sanda yana nufin barin gida cikin koshin lafiya, kada ka taba tabbatar da dawowarka,” in ji rundunar ba tare da bayar da cikakken bayani kan yadda aka kashe dan sandan ba.
Kisan dai ya faru ne watanni biyu bayan wasu ‘yan bindiga sun kashe wani ma’aikacin a yayin da suke gudanar da bincike a garin Fatakwal, babban birnin jihar Ribas.