fidelitybank

‘Yan bindiga sun kashe mutum 5 harda mai shekaru 120 a Sokoto

Date:

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Raka da ke karamar hukumar Tangaza a jihar Sokoto, inda suka kona gidaje da kayan abinci da dama kafin su tafi da wasu dabbobin gida da ba a bayyana adadinsu ba.

DAILY POST ta tattaro cewa ‘yan fashin sun kashe wata mata ‘yar shekara 120 da wasu mutane biyar.

Da aka tuntubi Hakimin yankin, Alhaji Sa’idu Wakili ta wayar tarho, ya tabbatar da faruwar harin, inda ya ce duk da cewa ba a yi garkuwa da kowa ba, ‘yan bindigar sun kona kashi biyu bisa uku na gidaje da kayayyakin abinci da kuma satar shanu.

Ya bukaci gwamnatin tarayya da na jihohi da su kara zage damtse wajen magance matsalolin tsaro a yankin.

Hakimin ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni da su samar da gagarumin hanyoyin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar yankin.

Shugaban riko na karamar hukumar Tangaza, Alhaji Ibrahim Lawal Junju, tare da mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin tituna, Engr. Mai Damma Tangaza ya ziyarci al’ummar garin tare da jajanta wa mutanen kauyen sannan kuma ya yi alkawarin mika sakamakon bincikensa ga gwamnati domin taimakon wadanda abin ya shafa.

Jaridar DAILY POST ta rawaito cewa babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin jihar ko kuma hukumomin tsaro har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

breaking news in nigeria today punch

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp