Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane uku tare da yin garkuwa da ‘yan mata biyar da kuma shugaban wata kungiyar ‘yan banga a Jalingo da ke jihar Taraba.
Lamarin ya faru ne a daren Asabar da Litinin a wurare daban-daban a cikin babban birnin.
An bayyana cewa an kashe wani mazaunin garin da wani dan sandan tafi da gidanka a tsakar dare a Lasandi, BabaYau da Sabongari.
Hakazalika, shugaban ‘yan banga, mai suna Bashir da ‘yan mata biyar, wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da su da misalin karfe 1:30 na safe a mahadar Saminaka a daren ranar Litinin.
Yankin dai na kusa da dajin Kwando ne a karamar hukumar Ardo-Kola ta jihar inda aka yi garkuwa da mutane 20 tare da kashe wasu mutane hudu ciki har da shugaban karamar hukumar a cikin ‘yan watannin da suka gabata. In ji Daily Trust.