‘Yan bidiga sun kai hare-hare a garin Nasarawar Godel na yankin karamar hukumar Birnin Magaji a jihar Zamfara.
Wannan dai shi ne karo na farko da ‘yan bindigar ke kai hari wannan gari, kamar yadda wani mutumin yankin da ya buƙaci a sakaya sunansa ya shaida wa BBC.
”Muna cikin halin farbaga da tashin hankali, inda ta kai ga wasu ba sa iya kwana a gidajensu, abin da ya faru jiya baƙon al’amari mu dai wajenmu, saboda ba mu taɓa fuskantar irin wannan hari ba”, in ji mutumin.
Ya ce maharan sun auka wa garin cikin gungunsu ɗauke da muggan makamai, inda suka kashe aƙalla mutum bakwai, tare da kashe wasu mutum uku a ƙauyen Dillashe mai maƙwabtaka da garin.
Mutumin garin ya shaida wa BBC cewa maharan sun kuma yi garkuwa da mutum aƙalla 15.
Maharan sun kuma ƙona gidajen mutanen garin tare da farfasa shaguna da ƙwashe dukiyoyi masu tarin yawa.
BBC ta kuma tuntuɓi kakakanin rundunar ‘yansanda da ɓangaren gwamnatin jihar Zamfara game da wannan harin, sun kuma ce za su bincika su sake kiranmu, amma har ya zuwa yanzu ba mu daga gare su ba.


