Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe manoma kusan tara a Unguwan Danko da ke kusa da kauyen Dogon Dawa a yankin Birnin Gwari a jihar Kaduna.
Rahotanni na cewa an kashe manoman ne da yammacin ranar Asabar a lokacin da suke aikin gonakinsu.
A cewar wata majiya, ‘yan bindigar sun tafi ne tare da wasu manoma uku zuwa inda ba a san inda suke ba.
Shima zababben dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kakangi Yahaya Musa ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa duk wadanda aka kashe manoma ne, yayin da wadanda suka samu raunukan harbin bindiga a yayin harin an garzaya da su asibiti domin yi musu magani.
A cewarsa, “Eh an tabbatar min da ranar Lahadi cewa ‘yan bindiga sun kashe manoma tara a Unguwar Danko kusa da kauyen Dogon Dawa a ranar Asabar da yamma, wasu kuma suka samu raunuka.
Ya bayyana cewa wasu daga cikin mutanen kauyen sun samu raunuka a lokacin da suka fuskanci ‘yan bindigar.
DSP Mohammed Jalige, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ya yi alkawarin zai dawo da cikakken bayanin lamarin, yayin da gwamnatin jihar ba ta mayar da martani kan harin ba.