Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, sun kashe mutum 7 a kauyukan Gara da Gamji da ke gundumar Burra a karamar hukumar Ningi a jihar Bauchi.
An tattaro wadannan hare-haren na daban, sun faru ne a daren ranar Talata lokacin da ‘yan bindigar suka afkawa kauyukan a kan babura, suka kai wa marigayin hari tare da kashe shi.
Wani dan kungiyar ’yan banga a gundumar, wanda ya zanta da manema labarai, ya ce jami’an tsaron yankin da ke wurin ba za su iya jurewa ‘yan bindigar da ke dauke da makamai ba, wadanda ya ce ana zargin masu garkuwa da mutane ne, kuma dole ne su gudu domin tsira.
Majiyar ta kara da cewa maharan sun harbe hakimin unguwar Gara mai shekaru 50 mai suna Mai Anguwa Ali tare da wasu mutane biyar har lahira.
Ya bayyana sunayen sauran da ‘yan bindigar suka kashe da sunan Alhaji Ibrahim; Shuaibu Adamu; Yunusa Adamu; Umaru Sabo da Ali Aldo.
Wani mazaunin unguwar da bai so a bayyana sunansa ba, ya ce ‘yan bindigar sun yi awon gaba da shaguna a kauyen tare da kwashe kayan abinci da babura biyu.
An kuma tattaro cewa maharan sun kuma kashe wani jami’in tsaro na sa kai guda daya tare da raunata wani jami’in soji guda a kauyen Gamji a yayin wani artabu da sojoji.
A wani labarin kuma, wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da sanyin safiyar Laraba sun kai farmaki kauyen Yadagungume inda suka yi garkuwa da matar da diyarsu da kuma direban wani shahararren dan kasuwa a yankin mai suna Alhaji Lawan Maliya.
A halin da ake ciki, rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da faruwar hare-hare da kashe-kashen, inda ta sanar da cewa, rundunar ‘yan sanda da sojoji sun yi nasarar kashe uku daga cikin ‘yan bindigar a yayin wani artabu da bindiga.
Da yake tabbatar da kisan ta wayar tarho, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, SP Ahmed Mohammed Wakili, ya ce ‘yan bindigar, ya bayyana a matsayin ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyukan biyu da dama, inda suka yi ta harbe-harbe tare da kashe mutane bakwai a cikin lamarin.
A cewar SP Wakil, “Mun samu labarin cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari a kauyukan Kada da Gamji da ke karkashin gundumar Burra a karamar hukumar Ningi. Sun zo da yawa, suna harbe-harbe a kaikaice, sakamakon haka, an kashe mutane bakwai.
“Jami’an rundunar tare da hadin gwiwar sojojin Najeriya sun yi artabu da ‘yan bindigar, an kashe uku daga cikinsu, yayin da wasu kuma suka garzaya da su cikin daji tare da samun raunukan harbin bindiga.”
Ya sanar da cewa, a yayin aikin, wani soja ya samu rauni kuma an garzaya da shi wani asibiti da ba a bayyana ba, inda a yanzu haka yake samun kulawa.
PPRO ta lissafa mutanen da aka kashe da Ali Usman; Shuaibu Adamu; Yunusa Adamu; Ali Alton da Umar Sabo Ibrahim, dukkansu daga kauyen Gamji.
Ya ce a halin yanzu jami’an ‘yan sanda tare da hadin gwiwar sauran ‘yan’uwan jami’an tsaro da ’yan banga sun killace dazuzzukan dajin da ke yankin da nufin zakulo barayin.
A cewarsa, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Auwal Musa Mohammad, ya umurci kwamandan yankin da ya yi duk abin da ya dace da doka domin kamo wadanda suka aikata laifin.