fidelitybank

;Yan bindiga sun kashe mutane 41 a Katsina

Date:

Rundunar ‘yan sanda reshen Jihar Katsina, ta ce, ‘yan bindiga sun kashe mutum aƙalla 41 sakamakon kwanton ɓaunar da suka yi wa ‘yan banga a jihar.

Sanarwar da kakakin rundunar, SP Gambo Isah, ya fitar ta ce lamarin ya faru ne ranar Alhamis da dare lokacin da mayaƙan sa-kai suka tunkari ‘yan bindigar da zimmar ƙwato dabbobinsu da ɓarayin shanu suka sace.

Sai dai mazauna yankin na cewa adadin ya zarta hakan, inda wasu ke cewa an kashe mutum kusan 60.

Karanta Wannan: ‘Yan bindiga sun harbe alkali a kotun Imo

“A ranar Laraba da misalin ƙarfe 10:00 na dare, ‘yan ta’adda sun kai hari gidan wani mutum mai suna Alhaji Muntari da ke Unguwar Audu Gare a Kandarawa na ƙaramar Hukumar Bakori, inda suka sace shanu 50 da awaki 30,” in ji sanarwar.

“Daga baya a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 10:00 na dare, ‘yan sa-kai da aka haramta suka taru daga ƙauyuka 11 na Bakori kuma suka nufi ‘yan ta’addan don ƙwato dabbobin da aka sace. Sun bi sawunsu har zuwa dajin Yargoje.

“Abin takaici, sai ‘yan ta’addan suka shirya musu kwanton-ɓauna, suka kashe 41 daga cikinsu sannan suka raunata biyu.”

SP Gambo ya ƙara da cewa kwamandan rundunar na Malumfashi ne ya jagoranci tawagar ‘yan sandan da suka kwaso gawar mamatan, yana mai cewa yanzu haka samamen haɗin gwiwa na jami’an na gudana “don gano waɗanda suka aikata kisan”.

www.legit.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp