fidelitybank

Yan bindiga sun kashe mutane 4 yayn da suka y garkuwa da 39 a Abuja

Date:

Akalla mutane hudu ne aka kashe yayin da wasu 39 suka yi garkuwa da su a lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari a Kuduru, da ke karamar hukumar Bwari ta babban birnin tarayya Abuja, da kuma Garam da Azu, wasu al’ummomi biyu a jihar Neja.

A ranar Asabar, 23 ga watan Disamba, wasu ‘yan bindiga sun kai hari a unguwar Garam, da ke tazarar mintuna biyar daga Bwari, inda suka kashe wani Fasto da ke Cocin Redeemed Christian Church of God, tare da yin garkuwa da wasu 13.

A ranar Alhamis 28 ga watan Disamba, ‘yan bindiga sun sake kai farmaki garin Kuduru, wanda ke da iyaka da Garam, inda suka yi garkuwa da mutane 18.

Haka kuma a ranar Juma’a, 29 ga watan Disamba, ‘yan bindiga sun mamaye garin Azu, inda suka kashe mutane uku tare da yin garkuwa da wasu takwas.

Wata mazauniyar Garam mai suna Misis Juliana, ta ce a gidan farko da ‘yan bindigar suka shiga, sun nemi a ba su gidan da suka nufa.

Ta ce: “’Yan bindigar sun shiga gidan da bai dace ba, suka yi garkuwa da wasu yara maza biyu kuma daga baya suka kai su gidan da suka nufa.

“Lokacin da suka isa wurin, sai suka yi garkuwa da dangin baki daya, amma a lokacin da suke barin gidan, sai suka harbe mutumin (wanda suka auna), wanda Fasto ne a Cocin Redeemed Christian Church of God a gaban matarsa da ‘ya’yansu uku.

“An kuma kara da cewa a lokacin da matar ta fahimci cewa ta bar jaririn nata dan watanni shida a baya, sai ta nemi izinin ‘yan bindigar su je su dauki jaririn, kuma mace daya tilo a cikin ‘yan bindigar ta bi ta zuwa gidan.

“Duk da haka, lokacin da ‘yar fashin ta kasa hakuri, sai ta bar matar, ta shiga cikin sauran kuma ta tafi tare da sauran mutanen da aka sace wadanda adadinsu ya kai 13.”

An tattaro matar faston, malami ce a daya daga cikin makarantun sakandaren gwamnati da ke Bwari.

Wani ganau ya ce ‘yan fashin sun yi hanyar zuwa gidan wani jami’in soji, inda suka nemi matar da bindigarsa da kakin sa.

“Matar ta gaya musu cewa mijinta yana bakin aiki. Sai dai sun yi garkuwa da ‘ya’yansa biyu.”

Shaidanun gani da ido ya kara da cewa an yi garkuwa da mutane 13, yayin da wani dan limamin cocin Redeemed Church mai shekaru biyar da aka kashe, ‘yan bindigar suka yi watsi da su a bakin kogi saboda ya kasa haye kogin.

Jami’an ‘yan banga ne suka kubutar da yaron, inda suka bi sawun barayin.

Shaidanun gani da ido ya ce ‘yan fashin sun tuntubi iyalan wadanda abin ya shafa kuma suna neman naira miliyan 50 ga kowane mutum a matsayin kudin fansa.

vanguard news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp