‘Yan bindiga sun kai hari tare da kashe dakarun ‘yan banga huɗu a Jihar Anambra da ke kudancin Najeriya anar Alhamis.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin a Ƙaramar Hukumar Ihiala da misalin ƙarfe 2:55 na dare, kuma a daidai lokacin ne ta samu kiran gaggawa daga mazauna yankin.
Sanarwar da kakakin rundunar, DSP Ikenga Tochukwu ya fitar, ta ce dakarunsu sun yi nasarar kashe ɗaya daga cikin maharan bayan sun isa wurin.
“Sai dai miyagun sun kashe ‘yan banga uku, suka cire kan ɗaya sannan suka cinna wa gida biyar wuta ta hanyar amfani da bam na man fetur da kuma bama-bamai,” in ji sanarwar.
DSP Tochukwu ya ce sun yi nasarar hana maharan haddasa ƙarin fitina, inda suka fatattake su da kuma ji wa ƙarin wasu raunuka.
Jami’an tsaro da mazauna yankin kudu maso gabashin Najeriya na fuskantar hare-hare sakamakon ayyukan ‘yan ƙungiyar Ipob da ke son ɓallewa da kuma kafa ƙasar Biafra.