Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane akalla 20 tare da yin garkuwa da mutane da dama a yammacin Lahadin da ta gabata a lokacin da suka kai hari kan wasu musulmi da ke bikin Mauludi a garin Kusa da ke karamar hukumar Musawa ta jihar Katsina.
A cewar majiyar, maharan a yawansu, sun far wa mutanen da ba a san ko su waye ba ne da misalin karfe 11:05 na rana, inda suka jefa kauyen cikin rudani da bakin ciki.
Wani dan banga da ya tabbatar wa manema labarai mumunar harin ya ce ‘yan bindigar sun kewaye wurin da ake gudanar da bukukuwan Mauludin inda suka yi harbin bindiga a kan mahalarta taron, inda suka jikkata da dama tare da kama wasu da dama zuwa wani wuri da ba a sani ba. Kafin jami’an tsaro su amsa kiran gaggawar, maharan sun bace a maboyarsu. Bayan harin, mun gano gawarwaki 20 a cikin kauyen.”
Da yake tabbatar da rahoton, kakakin rundunar ‘yan sandan Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya ce. “Eh, an kai hari a karamar hukumar Musawa da misalin karfe 11 na dare a daidai lokacin da jama’a ke gudanar da Muzaharar Mauludi. ‘Yan bindiga sun kai hari inda suka harbe mutane 18 suka jikkata. An kwashe su zuwa asibiti domin yi musu magani. Daga baya, biyu daga cikinsu sun mutu. Ana ci gaba da gudanar da bincike don ganin an kama su tare da gurfanar da wadanda suka aikata wadannan ayyuka a gaban kuliya.