Rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina ta tabbatar da kisan mutane 11 da wasu ‘yan bindiga suka kai wasu kauyuka uku a karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Mista Abubakar Sadiq-Aliyu, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Katsina ranar Lahadi.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa Sadiq-Aliyu yana maida martani ne kan wani rahoto da ke cewa maharan sun kashe mutane 40.
“Muna sane da wani rahoto na yaudara da aka yi ta zagayawa, musamman a Facebook, cewa ‘yan bindiga sun kai hari kauyuka uku a Bakori tare da kashe mutane 40.
“Hukumar tana so ta fito fili ta karyata wannan ikirari a matsayin yaudara, kuma ta daidaita rikodin.
“A ranar 25 ga Mayu, 2024, ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Unguwar Lamido da ke Bakori inda suka harbe mutane 11 har lahira.
“Jami’an ‘yan sanda na Bakori da ya samu labarin, ya yi gaggawar tara jami’an tsaro tare da garzaya wurin da lamarin ya faru inda suka samu nasarar dawo da zaman lafiya tare da hana asara,” ya bayyana.
Ya bukaci jama’a da su yi watsi da rahoton na karya, ya kuma yi gargadi kan yada labaran da ba a tabbatar da su ba.
Ya shawarci jama’a da su rika tantance bayanai, ta hanyoyin sadarwa kafin a raba su domin yada labaran karya na iya haifar da firgici, tsoro da tashin hankali da ba dole ba.
Ya nakalto kwamishinan ‘yan sandan jihar Mista A. A. Musa yana jajantawa abokai da iyalan wadanda harin ya rutsa da su, yayin da ya yi Allah wadai da harin.
“Kwamishinan ya kuma ba da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da tura karin jami’ai don tabbatar da kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika.
“Kwamishinan ya kuma bukaci duk wanda ke da bayanai masu amfani da za su taimaka wajen gudanar da bincike da su fito su taimaka wajen gurfanar da wadanda suka aikata laifin a gaban kuliya.
“Ana ci gaba da gudanar da bincike; rundunar tana aiki kafada da kafada da masu ruwa da tsaki da sauran al’umma domin zakulo wadanda suka kai harin,” inji shi.