fidelitybank

‘Yan bindiga sun kashe mutane 10 a Zamfara

Date:

Rahotanni daga jihar Zamfara na cewa wani gungun ‘yan bindiga ya afkawa kauyen Kwanar Dutse da ke masarautar Dansadau da ke karamar hukumar Mulki ta Maru, a daren Laraba.

Mazauna garin dai sun ce ‘yan bindigar karkashin jagorancin gawurtaccen dan bindigar nan a yankin, Damuna sun afka musu ne saboda sun gaza biyan harajin naira miliyan ashirin da dan bindigar ya dora musu.

Jihar Zamfara na fama da hare-haren ‘yan bindiga da sace tare da garkuwa da al’umma domin kudin fansa, inda da wuya rana ta fito ta fadi ba a ji irin wadannan munanan labarin ba.

Wata uwa da aka kashe wa da ta ce “muna zaune muna gudanar da al’amuranmu kawai sai muka ji harbi. Sai muka kwasa da gudu, a inda ‘yan bindigar suka yi ta harbin kan mai uwa dawabi. Ina fatan za a sako min ‘ya’yana”.

Shi ma wani wanda mazaunin garin ne ya shaida wa BBC cewa ” yanzu haka akwai mata fiye da 50 da ke hannunsu a cikin daji”.

To sai dai gwamnatin jihar a ta bakin mai magana da yawun gwamnati, Sulaiman Bala Idris, ta ce ana samun sauyi sabanin yadda jihar ta Zamfara take a baya, “ina mamakin yadda jama’a ba sa fadar irin nasarorin da gwamnatin nan ke samu. Ko a shekaran jiya sai da aka kashe gagga-gaggan ‘yan bindiga”.

A watan Nuwamban badi dai wasu maharan sun yi garkuwa da kimanin mutum dari da suka hada da mata da yara daga garuruwan a matsayin mayar da martini sanadiyyar wani hari ta sama da sojoji suka kai a maboyarsu.

nigeria newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp