Wasu ‘yan bindiga sun kashe farfesa Yusuf Saidu, mataimakin shugaban sashen bincike da ƙirƙire-ƙirƙire da ci gaba na jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto.
Jami’ar ta sanar da rasuwarsa ne a wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, inda ta bayyana cewa wasu ‘yan bindiga ne suka kai masa hari tare da kashe shi a lokacin da yake kan hanyarsa daga Sokoto zuwa Kaduna.
“’Yan bindiga sun kai wa farfesa Yusuf Saidu hari tare da kashe shi a kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga jihar Sakkwato.” in ji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa “Yusuf Saidu mutum ne mai gaskiya da addini da sadaukarwa da kuma jaruntaka.”
Jami’ar ta bayyana rasuwar tasa a matsayin wani rashi mai radadi ga jami’ar da kuma daukacin al’ummar jami’ar, inda suka yi addu’ar Allah ya jikansa da rahama.
Sokoto dai na ɗaya daga cikin jihohin arewa maso yamma da ke fama da matsalar rashin tsaro da ƴan bindiga.