Wasu ‘yan bindiga a yankin Kudu maso Gabashi sun kashe wani shahararren malamin addinin musulunci a yankin mai suna Sheikh Ibrahim Iyiorji.
Politics Nigeria ta gano cewa, Sheikh Iyiorji ya rasu ne a daren ranar Litinin a asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya dake Abakaliki bayan wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai masa hari a gidansa da ke Isu a karamar hukumar Onicha ta jihar Ebonyi a daren Lahadi.
Da suke mayar da martani kan kisan malamin, mambobin kungiyar kare hakkin musulmi (MURIC) reshen Abuja, sun jajantawa al’ummar Musulmin Jihar Ebonyi.
A wata sanarwar hadin gwiwa da suka sanyawa hannu Salahudeen Ustaz Yunus, shugaban kungiyar MURIC reshen Abuja; da Luqman Leleye, jami’in hulda da jama’a na kungiyar MURIC reshen Abuja, kungiyar ta bukaci hukumomi da su gano tushen lamarin.
“Allah Ya baiwa gwamnati damar yin duk abin da ake bukata don gano tushen al’amuran da ke tattare da harin da shaidanun mutanen da suka kai masa harin.


