Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai hari a unguwar Ushafa da ke karamar hukumar Bwari a Abuja, inda suka kashe wani mutum tare da yin garkuwa da ‘yan uwansa.
Lmarin wanda ya afku a safiyar ranar Laraba da misalin karfe daya na safe ya tayar da hankula a yankin.
Wani dan unguwar, Mista James Olachi, ya shaidawa DAILY POST cewa, lamarin ya faru ne a bayan makarantar firamare ta LGEA Ushafa, kusa da sanannen wurin shakatawa na Going-park.
A cewar Mista James, maharan sun mamaye yankin kuma sun shafe sama da mintuna 30 suna harbe-harbe ba tare da katsewa daga wata hukumar tsaro ba.
Marigayin mai suna Mista Adegoke, an ce ya sha fama da masu garkuwa da mutane kafin a harbe shi.
Maharan da suka kai harin sun tafi da matar da wani dan uwansu zuwa inda ba a san inda suke ba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, DSP Josephine Adeh, ba ta amsa kiran wayarta ba, ko kuma ta amsa sakon tes da wakilin DAILY POST ya aike mata.