fidelitybank

‘Yan Bindiga sun kashe jami’in tsaro na sintiri 4 a jihar Anambra

Date:

‘Yanbindiga sun kashe ‘yan ƙungiyar sintiri ta tsaro na jihar Anambra huɗu a yau Litinin.

Uku daga cikin ‘yansintirin an kashe su ne a garin Ukpo da ke ƙaramar hukumar Dunukofia, yayin da ɗayan aka kashe shi a Abatete, da ke ƙaramar hukumar Idemili ta Arewa.

Jarida Daily Trust ta ruwaito cewa ‘yanbindigar sun yi dirar-mikiya ne a garin na Abatete, inda suka buɗe wuta suna harbin kan-mai-uwa-da-wabi, inda suka kashe mutum ɗaya.

Sun kai harin ne bayan da gwamnan jihar Charles Soludo ya bayar da umarni ga ‘yankasuwa su yi watsi da umarnin ‘yan haramtacciyar kungiyar a-ware ta Biafra na zaman gida a duk ranar Litinin, su ci gaba da harkokinsu.

Wani da ya ga yadda aka kai harin ya ce, bayan da ‘yanbindigar suka kashe ‘yan sintirin uku a Ukpo sai suka cinna wa motarsu wuta suka kuma kama mutum wajen bakwai suka tsere da su, tare da raunata wasu da dama.

Kakakin rundunar ‘yansandan jihar ta Anambra SP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma ya ce babban jami’in ‘yansanda na Ukpo na gudanar da bincike a kai.

A mako biyu da ya gabata Gwamna Soludo ya bayar da umarnin a riƙa buɗe dukkanin kasuwanni a jihar a ranar Litinin, wato a yi watsi da hanin da ƙungiyar ta IPOB ta yi.

general news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp