Wani shingen binciken jami’an tsaro na hadin guiwa da ke kusa da Bataliya ta 35 na sojojin Najeriya da ke kan titin Katsina zuwa Jibia ya fuskanci harin ta’addanci a ranar Alhamis, inda suka kashe jami’in kwastam a cikin lamarin.
A cewar wata majiya, ‘yan ta’addan da ke kan babura dauke da makamai, wadanda yawansu ya haura 40, sun kai farmaki kan shingen binciken ne da misalin karfe 2:00 na safiyar ranar Alhamis.
‘Yan ta’addan da ake zargin sun fito ne daga sansanin Solar da ‘yan ta’addan da aka kashe a baya-bayan nan, an ce sun shafe sama da mintuna 30 suna rike da madafun iko, inda suka kashe jami’in kwastam mai suna Abu Abbo sannan suka tafi da bindigarsa.
Majiyar ta ce karfin wutar da ‘yan ta’addan ke yi ya zarce na jami’an tsaro da ke kula da shingen binciken.
“Na tabbata wadannan ‘yan ta’addan sun zo ne don kawai su gwada yadda za su iya shiga sabon ginin hukumar gidan gyaran hali ta Katsina wanda ke fuskantar Barikin Sojojin Katsina kai tsaye.
Idan dai za a iya tunawa, kwanaki uku da suka gabata ‘yan ta’addan sun kuma kashe wani sifeton ‘yan sanda, Idris Musa tare da kona motarsa a kusa da Makera Quarters, a unguwar Kwakware da ke kan titin Katsina zuwa Jibia.