‘Yan bindiga su kimanin mutum biyar sun hallaka Daraktan ayyuka na hukumar bayanan jihar Kaduna KADGIS, Alhaji Dauda Anchau, a gidansa.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, ‘yan bindigan sun dira gidansa ne dake unguwar Barakallahu, karamar hukumar Igabi inda suka hallakashi.
‘Yan bindigan basu dauki komai a gidan sa ba, kawai kasheshi suka yi suka tafi. A cewar wata majiya mai tushe.
Dagacin garin, Alhaji Muhammad Abdullahi, ya tabbatar da labarin harin, inda ya ce, Baturan ‘yan sanda na unguwar Rigachukuwun da Barnawa sun ziyarci wajen
A cewarsa: “Wannan kisan kai ne kawai, saboda gidansa suka je, suka kashe shi kuma basu dauki komai a gidanba, kuma basu taba maigadinsa da matarsa ba. Ko daya kauyen da suka kai hari, ba a kashe kowa ba, kawai sun taba kura ne suka tafi. Sun yi hakan ne domin ayi tunanin unguwar suka kai hari.”Â