Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani tsoho mai shekaru 90 da kuma wasu mutane biyu a wani samame da suka kai daren Juma’a a jihar Gombe.
Da yake tabbatar da harin, kwamishinan ‘yan sandan Gombe, Mista Oqua Etim, ya ce an yi wa tsoho mai shekaru 90 da hadi da wasu mutane biyu kisan-kiyashi a lokacin da ‘yan bindiga suka kai harin, yayin da wasu uku da suka samu munanan raunuka aka kai su asibiti domin yi musu magani.
Ya ce dattijon yana barci sai ‘yan fashin suka cinnawa bukkarsa wuta. An ce an kona gidaje da shagunan abinci da dama yayin hare-haren.
Ya gargadi mazauna yankin da su guji yin barazana ga rayuwar jama’a saboda nasarorin siyasa inda ya bukace su da su saki siyasa daga aikata laifuka.
Ya shaida cewar harkokin siyasa na tafiya cikin kwanciyar hankali amma aikata laifuka a kowace al’umma abu ne da ke ci gaba da gudana kuma rundunar tana yin bakin kokarinta wajen yakar duk wani nau’in miyagun mutane a jihar.