Wasu ‘yan bindiga a garin Nsukka na jihar Enugu, sun kashe dan sanda tare da kona motocin sintiri a wasu wuraren binciken jami’an ‘yan sanda guda biyu da ke yankin.
Kamfanin dillancin labarai na kasaa (NAN) ya rawaito cewa, an kashe dan sandan ne a mahadar Umaru da ke Nsukka yayin da aka kona motar ‘yan sandan da ke sintiri a kan hanyar Ibeagwa-Ani a yankin.
Wani ganau a mahadar, Umaru wanda ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa NAN a Nsukka a ranar Juma’a cewa, da misalin karfe 6.20 na safe mazauna yankin suka fara jin harbe-harbe na bindigogi a yankin.
“Na garzaya zuwa ƙofofina don tabbatr da cewa dukkansu sun kulle sosai.
“Na kashe dukkan fitulun wutar lantarki a gidana kuma na gaya wa matata da ’ya’yana su yi shiru domin ina ganin ’yan fashi da makami ne,” inji shi.


